Dattawan Arewa da na Ibo sun yi alla-wadai da tafiye-tafiyen Tinubu

Spread the love

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya da takwararta ta Ohanaeze Ndigbo mai kare muradun al’ummar Igbo da wasu kungiyoyin farar hula sun bayyana rashin jin dadinsu game da tafiya zuwa Paris da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya yi daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro.

A ranar Laraba 24 ga watan Janairu ne shugaba Tinubu ya tafi zuwa Faransa domin wata ziyara ta kashin kai.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar gabanin tafiyar, ta ce Tinubu zai koma Najeriya cikin makon farko na watan Fabarairu.

Sai dai kungiyoyin a hirarsu da jaridar Daily Trust sun koka cewa babu gaskiya cikin sanarwar tafiyar la’akari da yadda aka kira tafiyar ta “kashin kai”.

Matakin kungiyoyin na zuwa ne bayan da shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki Tinubu inda ya bayyana shakku game da makasudin tafiyar tasa zuwa Faransa yayin da ake fuskantar karuwar matsalar yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke ci gaba da ta’azzara.

Sai dai Fadar shugaban kasar ta ce duk da cewa Tinubu ba ya kasar, yana aiki tukuru domin kawo saukin matsalolin kuma yana bai wa hukumomin tsaro dukkanin goyon bayan da suke bukata domin samun nasara kan masu aikata miyagun laifuka da nufin fitar da Najeriya daga halin rashin tsaron da take ciki.

Me kaddamar da dakarun sa-kai da jihohin arewacin Najeriya ke yi ke nufi?

Yan sanda sun ceto mutum biyu da aka sace a Abuja

Tinubu dai ya sa kafa ya fice daga kasar yayin da ake tsokaci game da jerin hare-haren da aka kai a Filato da sace-sacen jama’a a Abuja, babban birnin kasar da kuma hari na baya-bayan nan na sace dalibai da malaman makaranta a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Kungiyar dattawan arewacin Najeriyar ta ce tafiyar ta Tinubu zuwa Paris a irin wannan yanayi da ake ciki a kasar manuniya ce cewa shugaban ya dukufa ne wajen cimma kudurorinsa na kashin kai a maimakon bai wa yan Najeriya kwarin gwiwa a lokacin da suke bukatar hakan.

Daraktan yada labarai na kungiyar, Abdulazeez Sulaiman ya ce kungiyar tana ganin matakin na shugaban kasar na tabbatar da damuwar da ake nunawa cewa Najeriya ta fada cikin matsalar rashin shugabanci na gari da rashin nuna damuwa da tausayi.

A nata bangaren, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi allah-wadai da tafiyar ta shugaba Tinubu zuwa Paris a halin tabarbarewar tsaro da sauran kalubale da ake ciki.

Babban sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce bulaguron da Tinubu ya yi na zuwa ne a lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki.

Isiguzoro ya yi kira ga Tinubu da ya yi wa yan Najeriya bayani dalilin yin irin wadan nan tafiye-tafiye.

Shi ma shugaban kungiyar tabbatar da jagoranci na gari, GGT, Mista Tunde Salman ya ce da alama shugaba Tinubu ya bai wa wasu manyan jami’ai har da mataimakin shugaban kasa damar tafiyar da al’amuran.

Ya ba da misali da wani kwarya-kwaryan taro da aka shirya kan tsaro game da karuwar matsalar a arewacin Najeriya, inda mataimakin shugaban kasa da ministocin tsaro suka zama masu taka rawa sosai a taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *