Daukar Fansa: Yan daba sun farwa yan kwamitin tsaro a Kano

Spread the love

Ana zargin wasu yan daba da farwa yan kwamitin tsaron Kofar Na’isa Kano, a lokacin da suke gudanar da aikinsu a daren jiya Litinin.

Shugaban kwamitin tsaron Kafar Na’isa Abdullahi Isma’il Kofar Na’isa , ne ya tabbatar da hakan a wani sakon murya da aike wa da manema labarai.

Abdullahi Kofar Na’isa , ya zargi wani mai suna Yasayyadi da jagorantar matasan yan daban , bisa zargin da suke yi wa yan kwamitin tsaron da hallaka mu su dan uwa mai suna Abba Dan Snake.

Ba mu ne muka yi sanadin kaɗe saurayi da mota a Jibiya ba – Kwastam

Ya kara da cewa , yanzu haka batun zargin kisan Abba Dan Snake ya na gaban kotun Majistiri dake zaman ta a unguwar Normand Sland, karkashin jagorancin mai shari’a Halima A.B. Wali.

Ya ce matasan sun dauki wannan mummunan mataki ne, bayan da wani ma’aikacin kotu mai suna Salisu ya bayyana mu su cewar kotun ba zara yi mu su adalci a shari’ar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *