Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da a ba wakilin jaridar Daily Nigerian ta intanet a Najeriya, Umar Audu tsaro na shekara goma saboda binciken ƙwaƙwaf da ya yi, wanda a ciki ya bankaɗo yadda ake amfani da kuɗi wajen mallakar digirin bogi daga Jamhuriyar Benin.
Binciken Mr Audu ne ya bankaɗo harƙallar mallakar kwalin digirin ta bayan fage, da kuma yadda ake amincewa da su a Najeriya a hukumance.
A zaman majalisar a ranar Litinin, ɗanmajalisa Abubakar Fulata ne ya sanar da umarnin majalisar, sannan ya yi kira da Rundunar ƴansanda da ta tsaron masu farin kaya wato NSCDC da sauran jami’an tsaro da su tabbatar da tsaron Audu.
“Muna godiya tare da yaba jajircewar Audu. Muna kira ga Ministan Harkokin Cikin Gida ya tabbatar jami’an tsaron NCDC sun ba Audu tsaro da ma ƴansanda,” in ji Fulata kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito daga NAN.