Wani direban mota ya mika wa Rundunar Yan Sandan jahar Kano, Wata Jaka da ya tsinta Mai dauke da makudan kudi a cikin ta, akan titin Hadejia Road kusa da mahadar Dakata dake jahar.
Mutumin mai suna Safiyanu Mohammed, dan shekaru 36 a duniya mazaunin unguwar Rangaza ta karamar Ungoggo, a Jahar Kano, amma Dan asalin Garin Iyatawa karamar hukumar Rimi ta jahar Katsina, ya tsinci jakar ce a ranar 9 ga watan Augusta 2024, Inda babu wata shaida da za a iya gane Mai ita ko kuma tuntubarsa.
Cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ta Yaba Wa direban Bisa gaskiya da rikon amanar da ya nuna, na kawo jakar kudin ga hukumar Yan Sandan jahar.
- Yara 3 sun nutse a ruwa a ƙauyen Jigawa
- Kotu ta tura shugabannin zanga-zangar Katsina gidan yari wata ɗaya
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa yanzu haka Jakar kudin da aka tsinta , tana shelkwatar Rundunar dake Bompai, kuma duk Wanda ya san ta sa ce , zai iya zuwa domin bayar da gamshasshen bayani, ko kuma a kira nambar waya 07033093437.
Idongari.ng ta ruwaito cewa, Kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya yaba wa direban Bisa gaskiyar da ya nuna , Inda ya bukaci duk Wanda yasan kudinsa ne, ya zo da tabbatacciyar hujja don ya karba.