Doguwa Ya Fice Daga Jam’iyar APC

Spread the love

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Sanata mas’ud El-jubril Doguwa ya fice daga jam’iyyar a jiya alhamis.

Sanata Doguwa ya bayyana ficewar ta sa ne daga APC a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kano.

“Ina sanar da ku cewa mun dauki wannan matakin ne da yawun dukkanin masoya da magoya bayan mu, saboda munanan manufofin jam’iyyar APC na kuntatawa talakawa.

Sanata Doguwa ya ce sun shiga APC ne a tunaninsu tun da suna da goge kan harkokin siyasa, za a rika tuntubarsu don ba da shawarwarin da zasu ciyar da jam’iyyar da kasa gaba.

Idan har Siyasa zata zama haka ace yan siyasa da suke da kwarewa ba za a rika basu wani aiki da zasu yi amfani da gogewarsu ba wajen kawo cigaba, to sai muce kaicho.

Ya ce jam’iyyar APC ta basu kungiya saboda manufofin da gwamnatin APC take aiwatarwa wadanda suka sanya talakawa cikin mawuyacin hali.

Sai dai Sanata Doguwa bai bayyana jam’iyyar da ya koma ba, bayan sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC.

Sanata mas’ud El-jubril Doguwa dai dan karamar hukumar doguwa ne dake yankin Kano ta kudu a jihar kano Nigeria.

Daily News24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *