Doka Ba Ta Ba Wa Dan Sanda Damar Kama Uba Ba Idan Dansa Ya Aikata Laifi , AIG Ari Ali Muhammed.

Spread the love

AIG Ari Ali Muhammad

Mataimakin babban sufeton yan sandan Nigeria, dake lura da shiya ta daya (  jahar Kano, AIG Ari Ali Muhammed, ya hori jami’an yan sanda, su daina sanya kansu cikin abubuwan da bai kamata ba.

AIG Ari Muhammed, ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa jami’an yan sandan Lakca, a wajen shakatawa na manyan jami’an yan sanda dake unguwar Bompai Kano a ranar Alhamis.

 

Ya ce wanda aka samu yana bin yan daba, ko barayi da ma su garkuwa da mutane,don su ba shi kudi, ba tare ya sanarwar da yan sandan ba, zai fuskanci na kora sannan gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

‘’duk dan sandan da aka rudeshi da kudi ya bi yan daba, don a bashi kudi, amma bai sanarwa da jami’an yan sanda wajen da masu laifin suke ba , to shi kansa mai laifi ne’’ AIG Ari A. Muhammed’’.

Haka zalika ya dada jan kunnensu musamman wadanda suke aiki akan hanyoyi, da su kaucewa cin zarafin mutum ta hanyar mari ko jefa shi cikin mota ba tare da ya aikata laifin komai ba, ko kuma kamo uba idan dansa ya yi laifi, inda ya tabbatar da cewar doka bata bayar da wannan damar ba, domin ba a kama wanda bai aikata laifin komai ba.

Matamakin sufeton yan sandan ya kuma kai ziyara shelkwatar rundunar yan sandan jahar Kano.

Da yake nasa jawabin kwamishinan yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya ce cikin kwanaki 85 sun kama wadanda Ake Zargi da aikata laifuka Dubu daya da dari da sittin da hudu 1,164, da suka hadar da Yan Fashi da makami 41, masu Garkuwa da mutane 5, barayi 13, Dilolin kwaya 10, Yan Damfara 7 da kuma Yan daba 153.

Haka zalika Rundunar ta Kubutar da mutane 5 da aka Yi Garkuwa da kuma mutane 13 da aka Yi niyar Safarar su zuwa kasashen ketare , an kuma kwato bindigu , harsasai , Ababen hawa, Kayanaye da wukake da dai Sauran su.

A karshe ya ce babban sufeton yan sandan Nigeria IGP Kayode Adeolu Egbektokun, ya bayar da umarnin hukunta duk wanda aka samu da kaucewa ka’idar aikinsa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *