Dole Musulmi da Kirista su haɗu su goya wa Falasɗinawa baya – Fani-Kayode

Spread the love

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Cif Femi Fani-Kayode ya ce dole Musulmi da Kirista baki ɗaya su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen goya wa Falasɗinawa baya.

Ya bayyana hakan ne a taron Ranar Aƙsa da ƙungiyar wayar da kan Musulmi ta Muslim Awareness International (MAI) wanda ya gudana a Filin Wasa na ƙasa da ke Surulere a Legas.

Sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron sun haɗa da darakta a MURIC Farfesa Lakin Akintola da Sheikh Sheikh Dhikrullahi Shafi’i.

Fani-Kayode ya daɗe yana caccakar Isra’ila a kan kisan kiyashin da ya ce tana yi wa Falasɗinawa, sannan ya ƙara da cewa Musulmi da Kiristan Najeriya dole su goya wa Falasɗinawa baya a ƙoƙarin Isra’ila na mamaye zirin Gaza.

A cewarsa, “an kasha maza da mata da ƙananan yara. An kashe Musulmi da Kirista, an tarwatsa Masallatai da Coci-coci. Suna yunƙurin shafe komai ne,” kamar yadda muka kalato daga jaridar Daily Trust.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *