Dole Najeriya ta ci gaba da gyaran tattalin arziki da take yi tsawon shekara 15′

Spread the love

Bankin Duniya ya ce dole ne Najeriya ta ci gaba da yin tsare-tsaren da take kai a yanzu na tsawon aƙalla shekara 15, muddin tana son ɗorewar tattalin arzikinta.

Mataimaikin shugaban bankin, Mr Indermit Gill ne ya bayyana haka a wani taron tattalin arziki karo na 30 da aka yi a Abuja ranar Litinin.

Ya ce ya kamata gwamnati ta jajirce wajen ci gaba da tsare-tsarenta na yanzu domin shawo kan matsaloli da ƙasar ke fuskanta wanda kuma suka janyo rashin cigaba tsawon lokaci.

“Babu wani wayo da za a yi a batun gyaran tattalin arziki. Ya kamata Najeriya ta tsaya kan tsare-tsarenta na tsawon shekara 15. Tsare-tsaren da aka ɗauka yanzu ba za su yi daɗi ba ko kuma kawo sakamako mai kyau nan take, amma za su ɗora ƙasar kan turbar cigaba mai ɗorewa,” in ji shi.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin ƴan Najeriya ke ci gaba da nuna fushinsu kan cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi da kuma tashin farashin dala.

Duk da cewa waɗannan tsare-tsare sun janyo tsadar rayuwa da kuma wahalhalu daban-daban ga ƴan ƙasar, jami’in na Bankin Duniya ya ce komawa baya ba zai haifar da ɗa mai ido ga tattalin arzikin ƙasar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *