Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta kada kuri’ar amincewa da umurtar Isra’ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan ƙare dangi a Gaza.
Alƙalan kotun sun kaɗa ƙuria’a 16 kan cewa akwai bukatar Isra’ila ta dauki dukkan matakan da suka dace na hanawa tare da hukunta wadanda ke da hannu wajen haddasa kisan kiyashi kan Falasdinawa a Zirin Gaza.
Har ila yau, ta hanyar kuri’a 16, kotun ta ce dole ne Isra’ila ta dauki matakan gaggawa don tabbatar da samar da agajin jin kai da na yau da kullun da ake bukata cikin gaggawa.
Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.