Dole sai an haɗa kai domin samun zaman lafiya a Najeriya – Jonathan

Spread the love

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya yi wani gargaɗin cewa ana buƙatar haɗin-kai tsakanin ‘yan Najeriya, domin samun zaman lafiya.

Jonathan ya ce yadda ƴan ƙasar ke fifita kabilunsu fiye da biyayya ga Najeriya na da matukar barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Tsohon shugaban ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sake duba abubuwan da suka sa a gaba da kuma ƙoƙarin samar da haɗinkai.

‘Biyayya ko fifita kabilanci na kawo cikas ga ci gaban Najeriya, don haka ya kamata shugabanni su aiwatar da manufofin da za su karfafa haɗin-kai maimakon neman suna ko yabo na kankanin lokaci,” in ji Jonathan.

Haka kuma ya nuna cewa akwai buƙatar sauya tunanin ƴan ƙasar, inda ya buƙaci ƴan majalisar tarayya da su ɗauki kowane ɗan Najeriya a matsayin nasu, ba wai ga jihohinsu ko kabilunsu kaɗai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *