Shugaban kasar Amurika Donald Trump, ya dakatar da shugaban hukumar raya kasashe ta kasar USAID, Paul Martin , kamar yadda kafafen yada labaran Amurika suka ruwaito A ranar Laraba.
An kori Poul ne bayan da ofishin ya fitar da rahoton sukar gwamnatin Trump kan kokarin rushe hukumar , kamar yadda Washington Post da CNN da sauran kafafen yada labarai suka ruwaito.
Rahotannin sunce an Aika da wasiku guda biyu ta hanyar Email, daga fadar White House da aka tura ranar talata zuwa ga martin inda aka masa cewa an soke mukaminsa ‘’ nan ta ke’’ amma babu wani bayani kan dalilin daukar hukuncin.
Haka zalika ofishin ya yi gargadin cewa fiye da Dala miliyan 489 na taimakon abinci suna fuskantar barazanar lalacewa ko karkatarwa bayan da gwamnatin Trump ta aiwatar da dakatar da taimako da kuma umarnin dakatar da aikin.
Gwamnatin Trump ta dakatar da taimakon kasashen waje, inda ta umarci dubban ma’aikata da ke aiki a kasashen waje su koma Amurka, kuma ta fara rage yawan ma’aikatan USAID daga 10,000 zuwa 300, tuni kungiyoyin kwadagon kasar suka kalubalanci matakin.
- USAID Ce Ke Daukar Nauyin Boko Haram Da ISIS: Scot Perry
- Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano