Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar cafke wasu daga cikin Yan fashi da makamin da suka addabi Unguwar Dorayi dake karamar hukumar Gwale a jahar.
Kwamishinan Yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a ziyarar da yankin Dorayin domin gana wa da Masu ruwa da tsaki, kan matsalar wasu batagarin Matasa da suka Hana al’umma zaman lafiya.
CP Gumel, ya yaba wa Dagacin Dorayi Karama, Alhaji Shehu Umar Sani, bisa jajircewarsa wajen wanzar da zaman lafiya a yankin sa.
- Jami’ar Khalifa Isiyaka Rabi’u, Ta Yaba Wa Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano
- Ana neman mutum takwas da ake zargi da kisan sojin Najeriya 17
Kwamishinan Yan sandan ya bayyana cewa, sunje yankin ne domin su fahimci juna tare da karbar shwarwari kan yadda za a magance matsalar, wadda ta faro kwanaki uku da suka gabata.
” babu Wanda bai San abunda yake daruwa a Unguwar Dorayi ba, wajen ba labari ne mai dadi ba” CP Gumel “.
A cewar a ranar Talata lokacin yana birnin tarayya Abuja, kuma a makonni Biyu da suka gabata sun taro kan matsalolin tsaro da jahohin da suke kewaye da jahar Kano, wadanda suka hada da Bauchi, Katsina, Sokoto, Zamfara Kebbi da kuma jahar Jigaa, inda aka tabbatar da cewar jahar Kano ce tafi kowaçce zaman lafiya.
Gumel ya ce daga ranar Laraba zuwa Alhamis sun kama yan fashi da makami 22, kuma ba za su yi wasa da al’amarin ba wajen gudanar da binciken kwakwaf.
Yanzu haka ya ce suna wasu mutane talatin , da ake zargin suna da hannu a aikata aika-aikar.
Jaridar Idongari.ng, ta wallafa sunayen wadanda rundunar yan sandan ke ma, da suka hada da, Duguja gidan Shanu, Baba Habu, Rigiji Tsamiyar Kuturu, Boris , Amiru Maye Yankifi, Yasari Gidan Gobirawa, Chasa Bakin Labi, Kanabaro Bakin Labi, Audu Magwaya, Nakwata Konannen gidan mai, Musa Kwata , Toti, Dan mafiçhi da kuma Riciever ( Risiba).
Sauran sune , Dan Hajiya Dorayi Sabis, Dantanda Dorayi Bakin Labi, Dan Mallam Dorayi Bakin Labi, Babba Dorayi Bakin Labi, Gundura, Nalutu, Malam Audu Dorayi Karama, Mai Kakari Dorayi Karama, Dini Gurgu, Mani, Alin Magashi , Abban Luwai, Tecno, Nasiru Babo da kuma Ahmed Ozil.
Rundunar ta ke duk Wanda ya San yasan su , ko kuma sunji da su garzayo ofishin Yan sanda domin tantance su, ko an bayar da sunayen su bisa kuskure.
Sai dai Kwamishinan ya ce mutane 30n da suka ambata suna son yin zaman gaggawa da su don samun zaman lafiya a yankin Dorayi.
Ya kuma godewa iyaye, ma su rike da masaratun gargajiya, da shugaban karamar hukumar hukumar Gwale , da kuma shugabancin kwamitin aikin tsaro da al’umma bisa hadin Kai da suke bayarwa akoda yaushe.