DPO Yaki karbar Cin Hancin N1m bayan ya kama Dan bindiga a Hotel

Spread the love

 

Wani Baturen ’yan sanda da ke kula da shiyar Tafa a Jihar Kaduna, ya yi fatali da tayin cin hanci na naira miliyan daya daga hannun wani dan ta’adda da ya kama.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, Manir Hassan ya ce, an yi kamen ne a otel din Easyway da ke Tafa a ranar 19 ga watan Janairun da muke ciki ne.

Ya ce DPO din garin Tafa ne ya jagoranci tawagar jami’ansa wajen kama dan ta’addan mai suna Bello Muhammad da ya fito daga Zamfara a wani otel da ke garin, inda suka same shi da kudin da ya kai naira miliyan biyu da dubu dari uku da hamsin da ake zargin kudin fansa ne daga garkuwa da mutane.

Hassan ya ce yayin bincike, Muhammad mai shekaru 28 ya amsa cewar shi mai garkuwa da mutane ne da ke gudanar da ayyukansa a dajin Kagarko da ke Jihar Kaduna, kuma kudin da ke tare da shi wani kaso ne daga cikin kudin fansar da suka karba.

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.

Yansanda sun kama mutum takwas da suke zargi da sace ɗaliban Ekiti

Jami’in ya ce a cikin wayarsa an gano hotunansa dauke da bindiga kirar AK47 wanda ‘yan sandan suka kwace, abinda ya sa ya yi tayín ba da naira miliyan guda ga DPOn domin kubutar da kansa, amma baturen ‘yan sandan ya ki.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna, A. D. Ali ya jinjina wa DPO’n da jami’ansa saboda wannan kokari tare da kiran su jajirce wajen kara kaimi a ayyukansu.

Kwamishinan ya kuma umurci masu kula da otal-otal, da sauran wuraren shakatawa a jihar da su rika sanya ido a kan kwastomominsu a koda yaushe domin kaucewa samar wa masu aikata laifuka mafaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *