Matasan jahar Gombe sun yi kira ga Dr. Jamilu isiyaku Gwamna, da ya fito takarar gwamna, a kakar zaben shekarar 2027, domin tada komadar fannonin rayuwarsu da suka durkushe.
A cewarsu babu wanda yake da kishin ganin al’umma sun samu ci gaba , don haka ne suke fatan ya fito ya nuna sha’awarsa, ta tsayawa takara, don inganta rayuwar matasa maza da mata domin sune kaso 70 na al’ummar Gombe.
Matasan sun kara da cewa , ba za su bashi kunya ba wajen yi masa ruwan kuri’u, tunda dai gamayyar matasa ne da suka hada maza da mata, kuma za su yi duk mai yiwu wa wajen tabbatar da nasarar sa.
Sun ce ba za yi kasa a gwiwa ba, wajen ci gaba da kiransa don ya amsa kiransu, tunda dai yasan matsalolin da matasan ke fuskanta , musamman abunda ya shafi rashin sana’o’in dogaro da kai , da hakan ke karawa yawan matasan ma su zaman kashe wando , da hakan ke kara yawan matasan dake shiga harkar shan kayan maye da miyagun laifuka.
Matasan sun kara da cewa Dr. Jamilu Gwamna, yasan hanyoyin da zai fito da su , idan Allah ya bashi nasara, don inganta rayuwar al’ummar jahar Gombe a fannoni daban-daban.