An samu sabani tsakanin wasu jami’an DSS da jami’an NSCDC da kuma masu gadin asibitin kwararru na jahar Edo a ranar Litinin.
Rahotanni na cewa , hatsaniyar ta samo asali ne bayan jami’an tsaron DSS din sun kai wani jami’insu Asibitin , sakamakon yanke jiki da yayi fadi a lokacin da suke gudanar da taro a ofishinsu.
jaridar idongari.ng ta ruwaito cewa, jami’an DSS din sun zargi jami’an kiwon kiwon lafiyar asibitin da sakaci da nuna halin ko in kula kan abokin aikin na su.
Daraktan asibitin Dokta David Odiko, ya ce lokacin da ya faru baya cikin asibitin sakamakon wani uziri da ya kaishi kotu , amma bayan zuwan sa ya samu labarin yadda lamarin ya kasance.
ya kara da cewa likitan dake bakin aiki ya duba shi , amma ya tabbatar ya mutu, sai dai jami’an DSS din sunki karbar gawarsa.
Bayan haka ne ake zargin jami’an hukumar tsaron farin kayan sun jiya jami’ar civil defence rauni a kanta, tare da wasu masu gadi sakamakon hatasaniyar da ta kaure a tsakanin su.
Jami’an yan sandan yankin karkashin baturen yan sanda na Oba Market Police Station sun kai dauki tare da sulhunta lamarin.
Sai dai har zuwa wannan lokaci rundunar yan sandan jahar bata yi karin haske ba kan faruwar lamarin ba.