DSS Sun Kama Mutum Da Jakunkunan Kudi Ya na Siyan Kuri’a A Jihar Ondo

Spread the love

Jami’an hukumar tsaro ta DSS a Najeriya sun kama wani mutum da ake zargi da sayen ƙuri’a a zaɓen gwaman jihar Ondo.

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa jami’an na DSS sun kama mutumin da jakankunan kuɗi da ake kyautata zaton zai yi amfani da su wajen sayen ƙuri’a.

An dai kama mutumin a rumfar zaɓe mai lamba ta 007 da ke makarantar furamaren St. Stephen a birnin Akure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *