Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta musanta wasu rahotannin da aka yada na cewa ta jibge jami’an ta a fadar Sarkin Kano, inda ta ce labarin ba gaskiya ba ne.
Daraktan DSS na jihar Kano, Muhammad Alhassan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Alhassan ya ce hukumar ta DSS ta tura jami’anta zuwa fadar sarkin saboda samar da tsaro sakamakon ziyarar da uwargidan shugaban kasa, Misis Oluremi Tinubu zata kai wa Sarkin.
- Ya kamata a riƙa sassauta wa mutane haraji – Muhammadu Sanusi ll
- Kotu Ta Yanke Wa ‘Yan Jarida Hukuncin Dauri A Gidan Yari Saboda Sukar Gwamnatin Tunisiya
Ya ce, daga baya an janye jami’a ne biyo bayan dage ziyarar saboda sarkin ba ya gari .
Ya ce babu gaskiya a cikin rahoton da ke cewa jami’an DSS sun yiwa fadar sarkin kano tsinke kan lamarin da ke faruwa a fadar gwamnatin jihar.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da rahoton na karya, wanda ya ce an yi shi ne don haifar ruɗani a cikin al’umma.
A ranar Alhamis ne Majalisar Dokokin jihar ta soke dokar Majalisar sarakunan Kano ta 2019, inda ta rusa masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano.
Kadaura24