DSS ta kama Bello Bodejo kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani

Spread the love

Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a jihar Nasarawa.

Wasu shuagabannin kungiyarsa ta Kautal Hore kuma makusanta sun tabbatar wa BBC da batun kama Bodejo a yau Talata.

Sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.

A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani

Bayanai na cewa jami’an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.

One thought on “DSS ta kama Bello Bodejo kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani

  1. Gaskiya bai kamata ace kasa kamar Nigeria a riƙa kafa kungiyoyi ire-iren wadannan ba ba don komai ba sai don kaucewa irin abinda ke gudana a kasar Sudan.
    Don Sudan ma daga kafa ire-iren wadannan kungiyoyi ne suka yi karfi har aka wayi gari yau suna fada da geamnati.
    Musamman kuma ace Fulani da yau
    da yawa daga cikin su suka zamo abin ƙyama sakamakon hare-haren ta’addanci da suke kaiwa al’ummar da basu ci ba basu sha ba musamman a arewacin Nigeria da ma sauran yankunan Africa.
    Wanda kowa yayi imani kungiyoyi da shuwagabanni na Fulani zasu iya taka muhimmiyar rawar gani wurin dakile ta’addancin ƴan’uwan nasu amma sunyi shiru, amma da zarar an taɓa nasu daya suna da bakin su fito suyi magana.
    Gaakiya idan Gwamnati tayi kuskuren basu izini to tamkar an buɗe ƙofar yakin basasa ne a Nigeria, domin kowacce kabila zata nemi izinin kafa Tata rundunar da hujjar kare kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *