DSS ta kama makusanciyar El-Rufai kan sukar gwamna Uba Sani

Spread the love

A ranar Lahadi ne jami’an tsaro da ake kyautata zaton jami’an tsaron farin kaya (DSS) ne suka kama wata mutuniyar El-Rufai kuma ‘yar siyasa da ke jam’iyyar APC a jihar Kaduna, Aisha Galadima.

Ana zargin kamen na da nasaba da wani saƙo da ta wallafa a shafin sada zumunta na facebook da ta yi wasu kalamai marasa daɗi ga gwamnan jihar, Uba Sani.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi sun nuna cewa Galadima ta bayyana rashin amincewarta da kalaman Sani na baya-bayan nan game da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Kamar yadda shaidu suka bayyana, an kama ta ne a unguwarsu da ke unguwar Tudun Wada da ke Kaduna a ranar Lahadi da yamma kuma wasu abokane sun bayyana cewa an kashe wayar ta bayan kama ta.

Sai dai kuma da aka tuntuɓi babban sakataren yaɗa Labarai na Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya game da kamen, kuma ya buƙaci ƙarin haske kan lamarin daga hukumar tsaro ta DSS

“Ba a sanar da ni cewa an kama wata ba da ta yi wasu kalami marasa daɗi gwamna Sani Uba ba, amma duk da haka, ya kamata a tuntubi hukumar ta DSS game da wannan batu, maimakon gwamnatin jihar Kaduna,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *