Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta ce ta kama wasu teloli da ake zargin suna ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano.
DSS ta ce mutanen na da alaƙa da tutocin da aka ɗinka wanda kuma aka rarraba a jihar.
Hukumar ta ce ta kuma kama waɗanda suka ba su aikin ɗinka tutocin, tana kuma ci gaba da bincike.
An dai ga ɗaruruwan masu zanga-zanga yawanci daga arewacin Najeriya rike da tutar Rasha
Ba a san dalilin kawo Rasha cikin zanga-zangar ba, to amma ana fargabar za a iya bai wa lamarin wata fassara ta daban.