Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, DSS ta saki wasu mutum bakwai da ta kama wata hudu baya yayin da suka koma ƙasar daga aikin Hajjin da ya gabata, bisa zargin zama ‘yan ta’adda.
Hukumar ta kuma bai wa kowannensu sallamar naira miliyan 1.
DSS ta ce ta sake su ne bayan kammala binciken da ta gudanar na watanni a kan zarginsu da zama ƴan ta’adda, kuma ba ta same su da laifi ba.
Mutanen wadanda sun kunshi Hausawa da Fulani sun hada da Al’amin daga jihar Oyo da Abdullahi Baba Komi daga jihar Kwara.
Lauyan mutanen Barista Bashir Sabi’u Ahmad, ya sheda wa BBC cewa ya ji dadi mutuƙa da matakin.
Wata majiya a hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin sababbin sauye-sauye da shugaban hukumar Adeola Oluwatosin Ajayi ya samar, a kokarinsu na sauya tunanin al’umma a kan yanda hukumar ke gudanar da binciken wadanda ake zargi da aikata laifi.