Duk Da Hada Layin Waya Da NIN Garkuwa Da Mutane Na Ci Gaba

Spread the love

Duk da hada layin waya (SIM) da lambar Katin Dan Kasa (NIN) na ’yan Nijeriya har yanzu matsalar tsaro a sassan kasar nan na ci gaba da ta’azzara kamar yadda wannan rahoto na Aminiya ya gano.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa rajistar da hada lambar wayarsu da ta NIN za su taimaka wa jami’an tsaro wajen kama ’yan ta’adda a kasar nan.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 26 ga watan Mayun 2021 ya bayyana gamsuwarsa da cewa hada layukan waya da na NIN na da matukar amfani wajen yaki da ta’adanci.

Festulation Foundation ta koyar da mata 50 sana’o’in dogaro da kai bayan sun warke daga larular yoyon fitsari a Kano

Buhari a lokacin kaddamar da tsarin tallata amfani da kayan cikin gida da kuma tsarin lambar NIN ta kasa a Abuja a wancan lokaci ya yi kira ga ’yan Nijeriya su goyi bayan hada layukansu da NIN.

“NIN zai taimaka wajen cike wani gibi a fannin tsaro, zai kuma taimaka mana wajen sanin hakikanin bayanan ’yan Nijeriya. Za mu gano mazauna ciki a saukake har da marasa gaskiya, “ in ji shi.

Buhari ya nuna cewa wannan tsari zai taimaka wajen inganta tsaro da tattalin arzikin kasa. “NIN tsarin kati ne na zamani a fannin sadarwa.

Kano: Hukumar KAROTA ta musanta wani rubutu da ta gani yana yawo da sunan ta

Kuma ’yan Nijeriya da doka ta amince masu dole su mallaki lambar ta musamman.

Hakan zai ba da damar amfana da gwamnati kuma zai taimaka wa gwamnatin wajen gudanar da tsare-tsaren tattalin arzikin kasa,” in ji tsohon Shugaban Kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *