Duk Dan Hisbar Da Bai Shirya Yin Aiki Tsakani Da Allah Ba Ya Ajiye Kakin Sa: Sheik Aminu Daurawa.

Spread the love

An bukaci kwamandojin Hisbah a kananan hukumomi 44 da su kara zage damtse wajen gudanar da aiyuka ma su nagarta, ta yadda jama’a za su ci gaba da amfana da aiyukan hukumar a birni da kar kara.

Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ne ya furta bukatar yin hakan a jawabin sa, a ya yin ganawa ta musanman da kwamandojin Hisbah da ke kula da aiyukan kananan hukumomi 44 a fadi jihar, a dakin taro na KERD a unguwar Gandun Albasa.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce duk dan Hisbah da bai shirya yin aikin Hisbah tsakaninsa da Allah ba, to ya ajiye kakinsa ya kara gaba, idan kuwa da gaske ya ke to, hukumar ta sa mi ci gaba, du ba da yadda aiyukan hukumar ke da muhimmanci a tsakanin jama’ar kano.

Babban kwamandan ya ci gaba da cewar domin bunkasa ilimin dakarunsa, tuni hukumar ta fitar da aiyukan Hisbah a aikace, kuma za’a fitar da tsare tsare guda 6 wanda hukumar za ta ci gaba da aiki a kansu, domin kai wa ga nasarar aiki.

Ya kara da cewar daga ciki a kwai kafa makarantar koyar da aikin Hisbah wato ( Hisbah Academy)

Kuma hukumar Hisbah za ta hada gwiwa da jami’ar Yusuf Maitama sule da jami’ar kwalejin ilimi ta sa’adatu Rimi da kwalejin sharia ta Malam Aminu kano da sashin yadda addinin musulunci na BUK, kuma za su bude cibiyoyin domin koyar da darusa akan aikin Hisbah da sauran su.

Ya ce za’a fadada aiyukan sashin ICT na hukumar ta yadda za’a zamanatar da sashin, ta yadda duk masu bincike ko neman bayani da sauran a kan aiyukan Hisbah za’a sa mu, a sauwake.

kuma ya ce a halin yanzu Hisbah ta karbi tallafin (computers) da sauran kayan aiki, dan fara fadada aiyukan sashin ICT dai da zamani.

Tun da fari a jawabansu da ban da ban, Babban mataimakin, Babban kwamanda, Mai kula da sashin aiyuka na yau da kullum, Dr. Mujahid Aminudeen Abubakar da takwararsa Mai kula da sashin mata Dr. Khadija Sagir Sulaiman, da Daraktan Mai kula da sashin Shari’un hukumar Hisbah sun bai yana cewar an shirya Taron ne domin yin ta za da tsifa a kan aiyukan hukumar, musanman a kananan hukumomi 44 .

Sun bukaci kwamandojin Hisbah na kananan hukumomi 44 da su kara kula da aiyukan su du da cewar an kafa hukumar Hisbah domin taimakawa sauran hukumomi wajen Samar da tsaro da zaman lafiya, wanda ya yi dai da koyarwan shari’ar musulunci a jihar kano.

Sun shawarce kwamandojin da suguji aiki da son ciya ko dan kare manufar wata jambiyar siyasa da sauran su, domin gujewa aikata da na sa ni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *