Tsangayar koyar da aikin jarida ta Jami’ar Bayero Kano, tare da hadin Gwiwar kungiyar ma’aikatan kafafen yada labarai ta kasa(SNB) sun shirya wa Yan Jarida bitar kara wa juna ilimi da kuma yadda Ake gudanar da bincike don bayar da rahoto na gaskiya.
Da yake gabatar da makasudin shirya Taron bitar, shugaban kungiyar ma’aikatan kafafen yada labarai na kasa farfesa Umaru Pate, ya ce sun shirya bitar ce kan yadda ake gudanar da bincike ta hanyar tsage gaskiya saboda mambobin kungIyar.
Pate ya kara da cewa dole ne Dan Jarida ya kasance Mai yin bincike gaskiya a duk lokacin da zai yada rahotansa don kar a Bata wa mutane suna.
“Wannan kungiya kullum ta na kokari kan yadda za a taimaki mambonin kungiyar “Pate”.
Ya Kuma ce duk kafar yada Labaran da ba ta kula da ma’aikacin ta ba, to Wani kula da shi a waje, Inda ya ja hankalin ma su kafafen Labaran su riga kula da hakkokin ma’aikatansu.
Haka zalika ya ba wa Yan Jarida shawarar cewa su Yi Aiki bisa kwarewa.
A nasa bangaren shugaban jamai’ar Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa gidauniyar MacAuthur ta tallafa mu su da makudan kudade musamman wajen samar da kayan sadarwa a Tsangayar Koyar Da Aikin Jarida da kuma horas da ‘yan jarida, inda ya kara da cewa sun kirkiro wasu sabbin sassa hudu a tsangayar don bai wa matasa damar samun koyon aikin jarida da rage rashin aikin Yi.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya ce daman kudirinsa shi ne bai wa ‘yan jarida horo a dukkan ma’aikatu na Gwamnati da masu zaman Kansu.
Gidauniyar MacAuthur ce ta dauki nauyin shirya bita ta kwanaki biyu wadda Ake gudanar wa a birnin Kano.