Ecowas na tunanin yadda za a sassanta da Nijar da Mali da Burkina Faso

Spread the love

Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) na shirin tattaunawa kan sassantawa da kuma shawo kan ƙasashen Burkina Faso da Mali da da ke ƙarƙashin jagorancin mulkin soja daga ficewa daga kungiyar a yayin taron su na gaba kamar yadda gidan rediyon Faransa na RFI ya rawaito.

Kotu ta yi umarnin likitoci su duba kwakwalwar Yar Tiktok Murja Kunya

Ana azumi kan tsadar rayuwa a jihar Borno

Ƙasashen uku sun buƙaci gaggauta ficewa daga kungiyar bayan bayyana aniyarsu ta ficewa daga kungiyar a ranar 29 ga watan Janairu.

“Muhimmin ra’ayinmu shi ne a tuntube su don su ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar,” in ji wata majiya da RFI ta ambato.

“Don cimma wannan…tattaunawar na iya kasancewa kan takunkumin da aka kakaba wa Nijar.”

Shugabannin kasashe irin su Faure Gnassingbe na Togo suna kira da a ɗage waɗannan takunkumin,” in ji RFI, inda ya kara da cewa “a halin yanzu babu tabbas”.

Rahoton na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka ruwaito shugaban hukumar ta Ecowas Omar Alieu Touray ya ce da wuya ƙungiyar ta bai wa ƙasashen yankin Sahel din uku damar ficewa daga kungiyar da wuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *