Ecowas ta nuna damuwa kan ɗage zaɓen Senegal

Spread the love

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta bayyana damuwarta kan matakin da hukumomin ƙasar suka ɗauka na ɗage zaɓen shugaban ƙasar da aka shirya gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Shugaban ƙasar, Mackey Sall ya danganta dalilin ɗage zaɓen da rikicin siyasa da ya kunno kai a ƙasar, wanda kuma ya sa aka hana da dama daga cikin ‘yan takarar tsayawa zaɓen.

Cikin wata sanarwar da Ecowas ta fitar ranar Asabar da daddare, shugabanninta sun yi kira ga hukumomin Senegal da su bi hanyoyin da suka dace, tare da sanya sabuwar ranar zaɓen.

Ecowas ɗin ta kuma umarci ‘yan siyasar ƙasar da su haɗa hannu, wajen tabbatar da gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a ƙasar.

Abubuwan da suka faru a zaben cike gibin karamar hukumar Kunchi Kano.

Sanarwar ɗage zaɓen da shugaba Salla ya yi, ya jefa al’ummar ƙasar cikin halin rashin tabbas, inda ‘yan adawa ke kallon matakin a matsayin tauye kundin tsarin mulki.

Ƙarƙashin dokokin zaɓen ƙasar, ana buƙatar aƙalla kwanaki 80 tsakanin lokacin da aka sanya ranar da aka sanya zuwa ranar zaɓen, kenan hakan na nufin lokaci mafi kusa da za a yi zaɓen ka iya kai wa ƙarshen watan Afrilu.

Senegal ba ta taɓa ɗage zaɓen shugaban ƙasa ba. Ta kuma gudanar da sauyin shugabancin farar hula cikin lumana har sau huɗu tun bayan da ta samun ‘yancin kai daga ƙasar Faransa a shekarar 1960.

Hakan kuma ya taimaka wajen ɗaga darajar ƙasar, wadda ta zama ɗaya daga cikin ƙasar da dimokradiyya ta wanzu a yankin Yammcin Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *