EFCC ta ƙwace unguwa guda daga wani tsohon jami’in gwamnati a Abuja

Spread the love

Hukumar EFCC ta samu nasarar ƙwace kadara mafi girma a tarihinta, inda a ranar Litinin, 2 ga watan Disamban 2024, mai shari’a Jude Onwuegbuzie ya mallaka wa gwamnati wani rukunin gidaje, wanda aka gina a fili mai faɗin murabba’in ƙasa 150,500, mai ɗauke da rukunin gidaje 753 da wasu gine-ginen a Abuja.

Wannan shi ne ƙwacen kadara mafi girma tun bayan kafa hukumar EFCC a shekarar 2003.

Kotu ta ƙwace rukunin gidajen ne mai lamba 109 a yankin Zone C09 da ke unguwar Lokogoma a Abuja, wanda kotun ta ce ta mallakin wani tsohon jami’in gwamnati ne, kamar yadda wata sanarwa da EFCC ta fitar ta nuna.

Da yake hukunci kan ƙwace rukunin gidajen, mai sharii’a Onwuegbuzie ya ce wanda ake ƙara ya kasa gamsar da kotun abin da zai hana a ƙwace masa kadarar, “wadda ake zargin ya mallaka da kuɗaɗen da ya samu ta wasu hanyoyi zamba. Don haka an ƙwace kadarar, an kuma miƙa ga gwamnatin tarayya.”

Tun da farko, a ranar 1 ga watan Nuwamban 2024 ne kotun ta fara ƙwace rukunin gidajen na wucin-gadi, kafin yanzu ta ƙwace baki ɗaya.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana cigaba da binciken jami’in gwamnatin

Shugaban hukumar, Mr Ola Olukoyede, ya sha nanata cewa ƙwace kadarorin da aka mallaka ta hanyoyi marasa kyau na da matuƙar muhimmanci a yaƙi da cin hanci da rashawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *