Shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin Hanci da rashawa a Najeriya, Ola Olukoyede ya ce hukumar ta samu nasarar ƙwato naira biliyan 156 daga ranar 29 ga waan Mayun 2023 zuwa 29 ga watan Mayun 2024.
Mista Olukoyede ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da wani shiri na musamman kan yaƙi da rashawa ranar Laraba a Abuja.
Ya ƙara da cewa daga kuɗaɗen da hukumar ta ƙwato sun haɗa da na ƙasashen waje da ma kudin intanet wato na kirifto.
Yayin da yake jawabi a madadin shugaban hukumar, sakataren EFCCn, Mohammed Hammajoda ya ce hukumar na nuna damuwarta kan yadda matasa da ɗalibai ke ƙara shiga harkokin damfara ta intanet da aka fi sani da ‘yahoo-yahoo’.
”Babu wani dalili da zai sa mutum ya shiga harkar yahoo-yahoo,” in ji shi.
Hukumar ta EFCC ta kuma ce ta kama kusan mutum 3,175 da laifi cikin shekara guda.
- Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga shida a Kaduna
- Rashin tsaro ya tilasta wa likitoci dakatar da aiki a asibitin yara na Kano