EFCC ta ƙwato naira biliyan 60 a cikin kwana 100 – Olukoyede

Spread the love

Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC, a Najeriya, Mista Ola Olukoyede, ya ce a cikin kwana 100, ofishinsa ya samu ƙorafe-ƙorafe 5,000 da suka danganci almundahana, kuma ya samu ƙwato N60bn.

A cewar shugaban, hukumar ta samu ƙwato wasu $10m, a wannan tsawon lokacin, kamar yadda wasu jaridun ƙasar suka ambato.

Haka kuma a cewar shugaban EFCC, hukumar ta samu nasarar yankewa mutane 700 hukunci, kan batutuwan da suka shafi kuɗaɗen da aka ƙwato, a ƙasa da watanni huɗu.

Ƙungiyar sanatocin Arewacin Najeriya za ta tura tawaga Nijar

Hedikwatar tsaro ta yi watsi da jita-jitar juyin mulki a Najeriya

Inda ya ƙara da cewa haɗa hannu wuri guda da al’umma na da muhimmanci, domin a cewarsa batun na da girma sosai ta yadda hukumarsa kaɗai ba za ta iya ba, sai al’umma sun taimaka wajen bayar da bayanai idan sun ga wani abu.

Mista Olukoyede ya bayyana cewa “idan har zan iya ƙwato naira biliyan 60 a ƙasa da kwana ɗari, me kake tunani game da yawan dukiyar da ake sacewa. “

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *