Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta kafa wani kwamiti kar takwana a dukkan ofishinta na shiyya a kasar, don dakile biyan kudin makaranta da dala, bayan faduwar darajar da naira ta yi a kasar.
Ta kuma ce ya gayyaci shugabanin jami’o’i masu zaman kansu da sauran manyan makarantu da ke kasar da ake biyan kudin karatun a makarantun da dalar Amurka.
Ƴan sandan sun kama waɗanda ake zargin sun shirya zanga-zanga a Neja
Yan sanda sun harbe dan bindigar da ke addabar Abuja
Wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC din Dele Oyewale ya fitar a yau Laraba ya ce kwamintin na kar ta kwana zai tabbatar da ganin an bi dokar hana lalata kudin kasa da amfani da dala a tattalin arziki.
Sanarwar ta kuma ce shugaban hukumar Ola olukoyede, wanda ya kaddamar da kwamitin kar ta kwana a Abuja, ya ce manufar smar da wannan kwamitin shi ne kare yadda ake cin zarafin tattalin arziki, da dukkan wasu wurare da kudde ke zurarewa.