Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa ta kama Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky saboda zargin sa da wulaƙanta takardar naira.
EFCC ta wallafa a shafinta na fesbuk cewa ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin damman takardun naira a bikin nuna wani fim da aka yi ranar 24 ga watan Maris a jihar Legas.
A baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.
A cewar hukumar, Bobrisky na ofishinta na Legas domin amsa tambayoyi.
EFCC ta ce ba da daɗewa ba za a gurfanar da Bobrisky a gaban kotu.
- Shari’ar Binance da Najeriya ya sami tsaiko
- ‘Hare-haren ƴan bindiga sun ɗaiɗaita mutum 289,375 a Kaduna’