EFCC ta kama manyan motoci 21 maƙare da kayan abinci

Spread the love

Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa ta’annati ta sanar da kama motocin dakon kaya 21 maƙare da kayan abinci da wasu kayayyaki da ke kan hanyar N’djamena a jamhuriyar Chadi da jamhuriyar tsakiyar Afirka da Kamaru.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, an kama manyan motocin ne yayin wani samame da aka ƙaddamar kan titunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a jihar Borno.

Binciken da aka gudanar ya nuna wasu kayan abinci da aka yi dabarar ɓoye su cikin motocin da za su iya wucewa ba tare da an gano ba.

Ƙarin binciken da aka gudanar ya nuna takardar da aka nannaɗe kayan da ke cikin motar ta nuna kayan za a kai su N’djamena a ƙasar Chadi da jamhuriyar Afirka ta tsakiya da kuma Kamaru.

Ba mu da niyyar yin katsalandan a dimokraɗiyyar Najeriya – Janar Lagbaja

Gwamnatin Enugu ta kashe kaji 30,000 a yayin rusau

Ana sa ran kamen motocin zai kawo ƙarshen matsalar abincin da ake fama da shi sakamakon yadda wasu ke fasaƙwabrinsa.

Ana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *