EFCC ta kama mutum 27 kan zargin zamba ta intanet a Bauchi

Spread the love

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya ta EFCC ta kama mutum 27 bisa zarginsu da aikata zamba ta intanet a jihar Bauchi da ke maso gabashin kasar.

Hukumomi a Kano sun cafke matar da ake zargi ta yi garkuwa da kanta a wani Hotel.

An kama ɗaliban Najeriya kan zargin zamba ta intanet

Cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce jami’an hukumar shiyar Gombe ne suka kama mutanen a ranar Alhamis 22 ga watan Fabrairu.

Hukumar ta ce jami’anta sun kama mutanen ne a wani otal da ke garin Yelwa a jihar Bauchi, bayan samun bayanan sirri kan zargin mutanen da aikata laifukan intanet.

EFCCn ta kuma kwato wasu abubuwa a wajen mutanen da suka hada da karamar mota kirar BMW, da wayoyin iphone da kwamfutoci da sauran manyan wayoyi.

Hukumar ta ce za ta gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *