Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC,Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta kama mutum 792 da ake zargi da aikata laifin damfara ta Intanet da suka gada da damfara ta hanyar soyayya.
An gabatar da wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 10 ga watan Disamba, 2024, yayin wani samame da jami’an hukumar suka kai a maɓoyar wadanda ake zargin, a cikin wani katafaren gini dake lamba bakwai, Oyin Jolayemi Street, Victoria Island, Lagos, bayan hukumar ta samu bayanan sirri.
Da yake jawabi ga manema labarai, Olukoyede, a ranar Litinin, 16 ga watan Disamba, 2024, a ofishin hukumar dake Lagos ya bayyana cewa cikin wadanda aka kama akwai yan Chana 148, da mutum 40 ƴan ƙasar Filipinos da kuma ƴan Kharzartans biyu, sai ɗan Pakistan da ɗan Indonesia.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Diraktan hulda da jama’a na hukumar, CE Wilson Uwujaren, ƴan ƙasashen wajen na amfani da ginin a matsayin wajen da suke koyar da ƴan Najeriya yadda ake damfara ta Intanet musamman ta hanyar soyayya, “Ƙasa a cikin ginin an cika shi da manyan kamfutoci”, in ji shi.
“A hawa na biyar, masu binciken sun gano layukan waya 500 da wayoyin sadarwa da aka tana da domin gudanar da ayyukan ta’addanci, ana amfani da ƴan Najeriyar wajen yaudarar ƴan ƙasashen waje yawanci ƴan Amurka da Canada da Mexico da wasu ƙasashen Turai da dama.
BBCH