Hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa ta kasa EFCC , ta kama tsohon Gwamnan Jahar Taraba, Darius Ishaku, bisa Zargin almundahanar naira biliyan N27bn, Wanda ya shafe shekaru 8, ya na mulkin jahar , kuma ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2023.
Rahotanni na cewa an kama tsohon Gwamnan Jahar Taraban a gidansa dake birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a.
Wata majiya Mai tushe ta tabbatar da cewa tsohon Gwamnan ya na tsare a hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC a daren juma’a , kuma za a Gurfanar da shi a gaban Kotu da Zargin tuhume-tuhume 15 kamar yadda majiyar ta tabbatar.
- Mene ne Gaskiyar Korar Seaman Abbas Daga Rundunar Sojin Nigeria Bayan An Sako Shi?
- Babbar Kotun Jahar Kwara Ta Yankewa Yan Fashin Bankin Offa Hukunci.