Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC sun kama shugaban cocin The Rock Ministry International, Apostle Theophilus Oloche Ebonyi, bisa zargin yi wa mabiya cocinsa da ‘yan Najeriya zamaba na tallafin kudin bogi daga Ford Foundation da kudin ya kai N1, 319,040,274.31 (Naira biliya daya d miliyan goma sha tara da dubu arba’in, da dari biyu da saba’in da hudu da kobo talatin da daya).
Wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar a yau Litinin ta ce an kama Mr. Ebony kan zargin damfarar masu tsautsayi da suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu na Najeriya da dai-dai ku, ta hanyar wallafa tallata wani aiaki da ake neman tallafi na kungiyarsa mai suna Theobarth Global Foundation, da ya ke da’awar cewar gidauniyar Ford za ta bashi tallafin dalar Amurka 20, 000 don taimakwa masu karamin karfi da ke cikin jama’a.
Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Bayelsa
Masu garkuwa sun sace fasinjojin bas kan hanyar Abuja
Haka kuma EFCC din ta yi zargin cewar ya nemi wadan da lamarin ya shafa da su yi rajisata tare da biyan kudin yin rajista, inda ya karbi N1,800,000 (naira miliyan daya da dubu dari takwas) kowannen su. ta wannan yarjejeniyar ne Mr Ebony ya tara N1,391,040, 274.31.
Hukumar ta EFCC ta ce bin ciken ta yi ta gano cewar babu wata yarjejeniya tsakanin Ford Foundation da Mr Ebonyi, sannan ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da shi a gaban kotu da zarar sun kamala bicike.