EFCC ta kama wasu mutum 40 da zargin damfara ta Intanet a Akwa Ibom

Spread the love

ami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC ta shiyyar Uyo sun kama wasu mutum 40 da ake zargi da damfara ta intanet a wani samame da suka yi da safiyar yau, Juma’a a wurare biyu daban-daban a jihar.

Hukumar ce ta sanar da hakan a shafin sada zumuntata na X.

Mutum 21 daga cikin mazan da ake zargin an kama su ne a garin Eket, yayin da sauran mutum 19 kuma a a Ikot Ekpene aka kama su.

Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da mota guda ɗaya da kwamfutocin tafi-da-gidanka guda tara da wayoyi 64 da kuma agogo mai kaifin basira

Hukumar ta ce za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *