EFCC ta musanta zargin far wa ƴan hamayya a Najeriya

Spread the love

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta musanta zargin zama ƴar amshin shatan jamʼiyyar APC mai mulkin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Talata, shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce zargin da jamʼiyyar adawa ta ADC ta yi cewa EFCC na harin ƴan adawa a ƙasar ba shi da makama kuma abin mamaki ne.

Olukoyede ya ce duk “wani mai bibiyar abubuwan da ke faruwa a Najeriya zai shaida cewa hukumar na gudanar da ayyukanta ba tare da son kai ba”.

”Kazalika iƙirarin ADC cewa ƴan tafiyar haɗaka sun samu sammaci daban-daban daga EFCC ba gaskiya bane”, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Hukumar ta kuma nemi ADC da sauran jamʼiyyun siyasa su mayar da hankali kan siyasarsu tare da bai wa hukumar damar yin aikinta.

A ranar Litinin ne jam’iyyar haɗakar da ADC ta zargi EFCC ta far wa ƴan haɗakar da nufin tsoratar da su.

Haka shi ma, Atiku Abubakar – jigo ne a tafiyar ta ADC – ya zargi hukumar da zama karen farautar jam’iyyar APC mai mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *