Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa a Najeriya ta soma binciken jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Bayanai sun ce ana zargin wata sakatariyar Kwankwaso, Folashade Aliyu ce ta shiga ta fita wajen yi wa uban gidanta sama da faɗin kuɗin jam’iyyar da suka haɗa da na yaƙin neman zaɓe da gudunmawar da jam’iyyar ta samu.
- Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 624 cikin watan Mayu
- EFCC ta ƙwato naira biliyan 156 a shekara guda
Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa, cikin korafin da Oginni ya gabatar, ana kuma zargin wasu ƙusoshin jam’iyyar ta NNPP a badaƙalar kuɗin da suka haɗa Farfesa Rufai Alkali, Abba Kawu da Dipo Olayokun.
“Ba abin mamaki ba ne idan hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa ta yanke shawarar bincikar Dipo Olayokun, dangane da yadda ya tara dukiya da mallakar kadarori a unguwannin masu alfama a birnin Abuja cikin ƙasa da shekara biyu na riko da akalar jagorancin masu lura da shige-da-ficen kuɗin jamiyyar NNPP.”
Da yake zantawa da jaridar Vanguard ta wayar tarho, Kwamared Oginni ya tabbatar da cewa ya amsa goron gayyatar Hukumar EFCC a Larabar makon jiya.
Ya ce ya ziyarci babban ofishin hukumar da ke Abuja inda ya gabatar da bahasi dangane da zargin karkatar da naira biliyan 2.5 da ake yi wa Sanata Kwankwaso.
A cewarsa, EFCC ta karɓi baƙuncinsa cikin mutuncin da karamci kuma ya tabbatar da zargin da ake yi wa jagoran jam’iyyar.
A halin yanzu dai wannan ya tabbatar da cewa EFCC ta tsunduma binciken zargin karkatar da kuɗin jam’iyyar NNPP da ake yi wa Sanata Kwankwaso, kuma nan ba da jimawa ba tana iya aika masa goron gayyata domin ya wanke kansa daga zargin.