EFCC za ta sa ido kan kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Spread the love

Hukumar EFCC ta ce za ta ƙarfafa bibiya tare da bin diddigin yadda ƙananan hukumomi suke kashe kuɗaɗensu a daidai lokacin da ake tunanin cin gashin kansu zai fara aiki daga watan Nuwamba, inda ake tunanin za a fara tura musu kuɗadensu kai-tsaye.

Tura kuɗaɗen kai-tsaye na cikin yunƙurin tabbatar da cin gashin kan ƙananan hukumomin guda 774 a Najeriya, lamarin da shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi na Najeriya, Hakeem Ambaliya ya bayyana wa jaridar Punch cewa suna farin ciki.

A ranar 11 ga watan Yulin bana ne dai Kotun Ƙolin Najeriya, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Garba Lawal, ta yanke hukuncin cewa ba daidai ba ne gwamnoni su riƙa karɓa tare da kula da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, inda ta buƙaci akanta-janar na ƙasar ya tabbatar ana tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu kai-tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *