Babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya buƙaci ƴansandan Najeriya su ɗaura baƙin kambi a hannunsu na tsawon kwana bakwai domin nuna jimamin rasuwar babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Kayode Egbetokun ya yi wannan kiran ne a wata sanarwa da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar.
- Yan sanda Sun Gargadi Al’umma Su Kara Kula Da Taransufomomin Su.
- Gwamnatin Kaduna ta bai wa masu zanga-zangar da aka saki kyautar wayoyi da kuɗi
“Bayan rasuwar babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban sufeton ƴansandan Najeriya Kayode Egbetokun ya buƙaci ƴansandan su ɗaura baƙin kambi a hannu na tsawon kwana bakwai domin jimamin rasuwar babban hafsan”.
“An bayar da umarnin ne domin alhini da girmamawa kan irin sadaukarwa da jajircewa da yaƙi da miyagun laifuka da ya yi. Shi ɗin babban jagora ne da ya dace da girmamawa ta ko’ina”.
Babban hafsan sojin ƙasan ya rasu ne a ranar Talata bayan fama da jinya.