Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya kai wata ziyara sakatariyar jam’iyyar SDP ta kasa da ke Abuja, a ranar Laraba.
SDP na daga cikin jam’iyyun da suka shiga zaben 2023, wanda El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa a cikin jami’yyar APC da ta yi nasara a jiharsa ta Kaduna da kuma matakin Shugaban Kasa.
Sunan Malam Nasiru na daga cikin wadanda aka mika wa majalisa domin tantnacewa a matsayin minista, sai dai bai samu sahalewar majalisar ba, sakamakon wasu dalilai da har yanzu ba a bayyana ba.
Bayan wannan tirka-tirkace El-Rufa’i ya yi batan dabo a siyasa, inda ba a kara jin duriyarsa ba a siyasance sai wannan ziyara da ya kai ofishin jam’iyyar SDP.
Ziyarar tasa ta soma yamutsa hazo, inda wasu ke alakanta ta da siyasar 2027.
Kotu Ta Kori Karar Da Ke Son A Hana Zabe Ranar Asabar A Najeriya
Yadda sojin Najeriya suka kashe ƴanbindiga da lalata maɓoyarsu