Endrick ya sharɓi kuka lokacin da Real Madrid ta gabatar da shi

Spread the love

Real Madrid ta gabatar da Endrick a gaban magoya baya ranar Asabar a Santiago Bernabeu, wanda ya ɓarke da kuka.

Ya ce dalilin kukan shi ne ”Tun ina ɗan yaro na ke mai goyon bayan Real Madrid, yanzu kuma na zama ɗan kwallon ƙungiyar.”

Filin ya ɗauki magoya baya da yawa har da ƴan Brazil da dama, waɗande ke dauke da rigar kasar da kuma ta ƙungiyar Palmeiras.

Fitattun tsoffin ƴan wasan Real Madrid sun halarci bikin tare da iyayen Endrick, haka shima mahaifin ɗan wasan, Douglas Ramos ya sha kuka a lokacin da zai zauna a kan kujera.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *