EndSars: Kotun Ecowas Ta Samu Gwamnatin Nigeria Da Laifin Ta Ke Hakkin Dan Adam

Spread the love

Kotun ECOWAS ta samu gwamnatin Najeriya da laifin take haƙkin wasu mutum uku a lokacin zanga-zangar lumana ta EndSar a 2020 a birnin Legas.

Kotun ta cegwamnatin Najeriya ta saɓa wa sashe na 1 da 4 da 6 da 9 da goma na kundin kare haƙƙin bil’adama na Afrika, musamman kan ƴancin rayuwa da kariya da faɗin albarkacin baki da na rayuwa da hana azabtarwa.

Masu shigar da ƙarar da suka haɗa da Obianuju Udeh da Perpetual Kamsi da Dabiraoluwa sun zargi jami’an tsaron gwamnatin Najeriya da take haƙƙinsu a lokacin zanga-zangar lumana ta EndSars a babbar gadar Lekki da ke birnin legas a ranar 20 ga watan Oktoban 20220.

To sai dai alƙalin kotun, Mai Shari’a Koroma Sengu ya yi watsi da zargin take ƴancin rayuwa na masu shigar da ƙarar.

Amma ya ce dole ne gwamnatin Najeriya ta biya kowanne a cikinsu naira miliyan 2 a matsayin diyyar take ƴancinsu na kariya da azabtarwa da na faɗin albarkacin baki da sauran ‘yancinsu.

Haka kuma alƙalin ya ƙara da cewa, dole ne gwamnatin ƙasar kamar yanda kundin kare haƙƙin bil’adama na Afrika ya tanadar ta yi bincike tare da hukunta jami’anta da ke da hannu a cin zarafin tare da kawo wa katu rahoton yadda ta aiwatar da hukuncin da kotun ta zartar a watanni shida masu zuwa.

Masu shigar da ƙarar sun zargin cewa a lokacin zanga zangar lumana – don kawo ƙarshen cin zarafin da jami’an ‘yan sandan SARS a babbar gadar Lekki a ranar 20 da kuma 21 ga watan Oktobar 2020 – waɗanda ake ƙarar sun aikata laifukan take haƙƙin bil’adama da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *