Faransa ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe bayan da ta yi nasara a kan Belgium da ci 1-0 ranar Litinin a fafatawar zagaye na biyu ta gasar Euro 2024.
Faransa ta ci kwallon saura minti biyar a tashi daga karawar bayan da Jan Vertonghen ya ci gida.
Da wannan sakamakon tawagar ta su Mbappe za ta jira wadda za ta fuskanta a zagayen daf da na kusa da na karshe tsakanin wadda ta yi nasara a wasan Portugal da Slovenia.
Za kuma su kara ne ranar Juma’a 5 ga watan Yuli a filin wasa na Volksparkstadion.
Portugal za ta kece raini da Slovenia nan da ‘yan mintuna a É—aya wasan zagaye na biyu.