Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya bada umarnin duk wanda ya fito harkar daba da masu tsaya musu ayi maganinsu ba tare da wani bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kakakin ‘yan sandan jihar SP Haruna Kiyawa ya fitar.
Kiyawa yace “A saboda haka, duk wanda aiki ya biyo ta kansa ba
kafa. An bawa Yan Sanda kayan aiki domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma ina fatan al’ummar jihar Kano zaku bamu hadin kai.
Yanzu haka, ana ta farautarsu duk wasu masu aikata munanan ayyuka da laifuka a fadin jihar.
“Duk mutumin da aka samu muggan makamai kamar Fate Fate, ‘Switzerland’, Dan Bida, Gariyo, a gidansa shima za a kamashi.