Fadan Daba Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Shahararren Dan Daba A Kano.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan jahar Kano ta tabbatar da mutuwar Shahararren Dan Daban nan da akafi Sani da Abba Bala Burakita, Wanda Ake Zargi da tayar da hankulan al’umma ta hanyar ji mu su raunuku da kuma kwace.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labari.

SP Abdullahi Kiyawa , ya ce sun samu kiraye-kiraye Daga kan titin zuwa gidan Gwamnatin Kano da kuma Unguwar Dorayi, kan cewa wasu Yan Fashi sun fito tare da Yi wa al’umma fashi da makami, inda Abba Bala Burakita ya jagoranci fashin da aka Yi kan titin zuwa gidan Gwamnatin Kano.

Burakita, dai ya yi ƙaurin suna wajen harkar daba, fashi da makami, ƙwace, sara-suka da sauran miyagun laifuka.

A baya dai Abba Burakita ya mika wuka ga rundunar yan sandan jahar Kano, inda suka ajiye makamansu shi da yaransa 40, har gwamnatin jahar horas da wasu sana’o’in dogaro da kai.

Haka zalika akwai Wani Mai suna Halifa Duguja, Wanda ya jagoranci fadan daba a unguwar Dorayi, Inda Inda suka ringa farfasa dukiyar al’umma .

Kwamishinan yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin tsare ko’ina, Inda tarar cewar Abba Burakita sun Yi fada da wasu gungun Yan daba har aka raunata shi a sassan jikinsa.

Daman dai tuni al’umma suka shigar da korafe-korafe kan Abba Burakita, kan Zargin Fashi da fadan daba, kuma bayan an Kai shi asibiti likita ya tabbatar da mutuwarsa.

One thought on “Fadan Daba Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Shahararren Dan Daba A Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *