Fadan Daba: Yan Sanda Sun Cafke Mutumin Da Ake Zargi Da Kisan Jami’in Bijilanti A Kano

Spread the love
SP Abdullahi Haruna Kiyawa Kakakin Yan sandan Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke mutum daya daga cikin ƴan dabar da ake zargin sun kashe kwamandan ƙungiyar Bijilante na unguwar Ja’en dake jihar Kano, mai suna Muhktar Garba, wanda akafi sani da Baballiya.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan.

Kiyawa ya ce bayan samun rahoton faruwar faɗan dabar a tsakanin ƴan unguwar Ja’en Maƙera, da kuma wasu ƴan unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, ne aka tura jami’an ƴan sanda don su samar da tsaro a yankin.

“Daga rahotannin da muká samu faɗa ne na ƴan Daba, da ya kaure a tsakanin ƴan unguwar guda biyu a daren ranar Talata, inda ƴan dabar suka rufe kwamandan Bijilanten da sara da makamai har ta kai ga sun yi masa illa bayan an kai shi Asibiti ya rasu, “in ji Kiyawa”.

Ya kuma ce zuwa yanzu akwai wani mutum ɗaya daga cikin ƴan dabar da aka gane shi kuma yana hannun ƴan sanda a babban sashin binciken manyan laifuka ɓangaren kisan kai ana faɗaɗa bincike.

SP Kiyawa, ya ƙara da cewa rahotannin da suka samu daga jami’an su yanzu haka komai ya fara dai-dai ta ƙura ta lafa, inda mutane suke gudanar da al’amuran su na yau da kullum.

A daren Talata ne aka zargi wasu ƴan Daba daga unguwar Ja’en Maƙera, suka shiga unguwar Ja’en Ƴan Dillalai, inda suka haifar da faɗan Daban, lamarin da har suka kashe kwamandan Bijilanten na Ƴan Dillalai, wanda tuni akayi jana’izar sa a jiya Laraba.

DALA FM.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *