Fadan Daba: Yan sandan Kano sun shiga unguwannin yan daba 72 tare da shelanta neman su a gaban al’umma.

Spread the love
Unguwannin birnin Kano

Rundunar yan sandan jahar Kano , ta gudanar gangamin wayar da kan jama’a, a wasu daga cikin unguwannin jahar, tare da sanarwa da al’umma, sunayen matasa 72 da rundunar ta ke nema kan zargin dawo da fadan daba, fashi da makami, kwace da kuma sace-sace.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne , ya bayyana hakan a tattaunawar da ya yi da Idongari.ng, a ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, duk wanda yake cikin birnin Kano yasan yadda wasu batagarin yan daba, da suke fitowa su tayar da fadan daba, don su tsorata mutane tare da razana su , inda suke yin sata da kuma kwace.

Dakarun yan sandan Kano

Hakanne ya sanya kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tara dakarun yan sanda , domin shiga unguwannin tare da yin sanar da sunayen matasa guda 72, wadanda ake zargi dumu-dumu a ta’addancin da ake yi.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce dukkan wadanda ake zargin kowa an shiga unguwarsa domin sanar da al’umma cewar rundunar tana neman su ruwa a jallo.

Wuraren da ake zargin sun addaba, sun hada da Dala, Gwale da wasu yankuna a karamar hukumar Fagge.

Tuni dai al’ummar yankunan da aka shiga dan wayar mu su da kai, kan neman matasan yan daban 72, sun bayyana jin dadinsu da irin namijin kokarin da yan sandan ke yi a koda yaushe.

Sai dai rundunar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da ba wa rundunar hadin kai, domin dakile aiyukan batagari da kuma kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan ya gargadi ma su son hana al’umma zaman lafiya, dan yin ta’addanci, fadan daba, kwacen waya, ko Rigima dan a zalinci al’umma da yi mu su asarar dukiya , ya tabbatar da cewa ba za su bari ba ayi ba, kamar yadda doka ta ba su dama sashe na 4, police Act 2020 da aka sabunta.

Sunayen yan dabar sun hada da

  No Sunaye Unguwa
1. Bahago Afah Kuka Bulukiya
2. Malam Keya Dogon Nama
3. Habu Mayo Kuka Bulukiya
4. Dan Mama Adakawa
5. Alhajin Bilal Lungun B/malam Madabo
6. Buda Karofin Dala
7. Alhaji Baba Shirawa
8. Abba Gashi Gashi Dandinshe Tasha
9. Hassan Cisse Rijiya Biyu
10. Dan Kamsusi Dandinshe
11. Likuman Makafin Dala
12. Saddiku Style Gadar Salga
13. Kwaja Dandinshe
14. Malam Rodi Dala Makarantar Nafahatu
15. Halifa Dan Asabe Shatsari
16. Bagiya Shatsari
17. Abba Ali Mugu Sanka
18. Dan Kyahun Rijiya Biyu
19. Nabara’u Madigawa
20. Habu Udukul Madigawa
21. Fato Madigawa
22. Haruna Musa Jibrin Madigawa
23. Malam Shehu Madigawa
24. Dahuwa Chediya
25. Fiya Dandinshe
26. Dubulliya Aikawa
27. Sharu Sharna Rijiya Biyu
28. Bukari Tijjani Dala
29. Dan Auwalu Kwanar Dala
30. Dan Chaina Kul-kul
31. Shangwa Rimin Abba Kul-kul
32. Dan Yellow Chediya
33. Abba Kan Fulogi Rijiya Biyu
34. Dilin Dala Layin Sarka Gurgu
35. Dandolo Lungun Kotu
36. Master Lungun Kotu
37. Dogo Kantin Uba Angwaye Titin Alfanda
38. Bala Kwalli Kantudu
39. Ala Baka Bakin Kasuwa Maskwani
40. Ummo Lungun Kotu
41. Walidi Lungun Yankifi
42. Guguwa Yalwa
43. Bisi Yalwa
44. Yartakabiruwa Yalwa
45. Ubaidu Kantudun Madabo
46. Shatoli Filin
47. Dan Isa Shirawa
48. Kabiru KB Show Bayan Dala Lungun Nafahatu
49. Nurere Lungun Kotu
50. Abba Ho Filin Faroma
51. Saddiku Savio Filin Kutare
52. Wando Filin Kutare
53. Yahaya Army Lungun Nafahatu
54. Mubarak Bade Lungun Nafahatu
55. Dan Umar Ziri Zirin Gyaranya
56. Abdul Lokon Makera Shatari
57. Addahir ( Dahri) Dirimin Daje
58. Tere Dirimin Daje
59. Annani Karofin Daganda
60. Tata Kantudu
61. Dan Sani Falo
62. Oris Kantudu
63. Tsulum Lungun Kankarofi
64. Mamman Kantudu
65. Malo Kantudu
66. Al-amin Makafin Dala
67. Tulu Dala
68. Abba Idan Dala
69. Tahani Lungun Yan Kifi
70. Kilo Dala
71. DaN Jamilu Adakawa
72. Dan Turkwi

IDONGARI.NG

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *