Fadar Sarakuna Ba Gurin Ajiyar Motoci Ba ne: Kwamishinan Yan Sandan Kano.

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta umarci wadanda suke ajiye Motocin su, a masarautun Kano, su dauke su ba tare da bata lokaci ba.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan a wajen taron karbar shawarwari daga Sarakuna da malamai don tabbatar da an gudanar da bukukuwan karamar Sallah lafiya.

CP Gumel , ya ce sun dauki matakin ne bayan karbar korafin Wakilin Sarkin Karaye , inda ake tara motoci a fadar dake kusa da ofishin Baturen yan sandan yankin.

Jaridar Idongari. ng, ta ruwaito cewa, daukar matakin ba zai rasa nasaba da yanayin tsaron da ake fuskanta a makotan jahohin jahar kamar Kaduna, Katsina, Zamfara, Sokoto, Naija, Bauchi da dai sauran su .

CP Gumel, ya Kara da cewa tuni suka raba nambobin wayar Neman daukin gaggawa, a dukkan fadin jahar Kano.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, ya godewa Sarakunan Kano, da Malaman addini bisa hadin kan da suke bayarwa akoda yaushe.

Makasudin Shirya taron shi ne , samun shawarwarin hanyoyin da za a bi wajen dakile dukkan Wata barazana ,ta masu yunkurin aikata laifuka yayin gudanar da bukukuwan karamar Sallah da ba ma bayan ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *